Yadda Ake Kare Kai Daga Hacking din WhatsApp

Gabatarwa

WhatsApp ya zama ɗaya daga cikin manhajojin sadarwa da aka fi amfani da su a duniya. Muna amfani da shi wajen:

  • tattaunawa da iyali da abokai
  • kasuwanci da ciniki
  • karɓar labarai da bayanai

Sai dai, tare da wannan amfani, damfara a WhatsApp na ƙara yawaita. Mutane da dama suna rasa kuɗi, bayanai, ko kuma ana satar accounts ɗinsu saboda rashin sani.

Wannan rubutu zai bayyana yadda damfara ke faruwa a WhatsApp da kuma hanyoyin kare kanka cikin sauƙi.

Menene Damfara a WhatsApp?

Damfara a WhatsApp na faruwa ne idan wani:

  • ya ruɗe ka da ƙarya
  • ya sa ka bayar da bayanan sirri
  • ko ya sa ka tura kuɗi ba tare da gaskiya ba

Yawanci masu damfara suna amfani da:

  • sakonnin gaggawa
  • alkawarin samun kudi ko taimako
  • tsoratarwa ko tausayi

Nau’o’in Damfara da Ake Yawan Yi a WhatsApp

1. Sakon “Canza Lamba”

Wani zai turo maka sako ya ce:

“Ni ne wane, na canza lamba, ina buƙatar taimako na gaggawa sabida ina cikin wani hali.”

Da zarar ka amsa, zai nemi kuɗi ko wani bayanai game dakai, kana yarda daka shikenan ya gama dakai.

👉 Gargadi: Abu na farko da zaka fara yi shine; Ka kira tsohon lambar wayan mutum don tabbatarwa kafin ka yarda.

2. Damfarar Tallan Kuɗi

Ana tura saƙonni kamar haka:

  • Sai acewa mutum “zuba kudi kaɗan ka samu riba mai yawa”
  • ko a turowa mutum cewa ga wani remote jobs da ake samun kudi sossai ka cike “aiki kana gida ka samu kuɗi” ba kuma muna cewa babu remote jobs bane, amma mafi yawancin su scam ne. musamman wanda za aturowa mutum ko a tallatawa mutum

Yawanci waɗannan ba gaskiya ba ne.

👉 Ka tuna: Babu kuɗin da ake samu cikin sauƙi ba tare da anyi aiki tukuru ba.

Wasu sakonni na zuwa da link kamar:

  • kyauta
  • tallafi
  • sabunta account

Da zarar ka danna, za a iya:

  • satar bayananka
  • ko mutum ya shigar da virus a wayar sa, ba tare da ya saniba

👉 Kada ka danna link da baka sani ba ko baka tabbatar da shiba.

4. Damfarar Lambar Tabbatarwa (Verification Code Scam)

Wani zai ce:

“Na turo maka nayi kuskure na turo maka wasu lambobi da Allah taimaka ka aiko min su ko ka fadamin su.”

Wannan lambar ita ce WhatsApp verification code ɗinka. ko facebook dinka, sabida kada aika:

  • za a sace account ɗinka.

👉 Kada ka taɓa bawa wani verification code dinka.

5. Kwaikwayon Hukuma ko Kamfani

Masu damfara suna kwaikwayon:

  • banki
  • kamfanin sadarwa
  • wata hukuma

Suna neman ka:

  • sabunta bayanai
  • aika OTP ko PIN

👉 Hukuma ta gaskiya ba ta neman bayanai ta WhatsApp.

Alamomin Da Zaka Gane Damfara a WhatsApp

Ga wasu alamomi:

  • saƙo mai cike da gaggawa (“yanzu-yanzu”)
  • alkawarin riba mai yawa
  • rubutu mara tsari ko kurakurai
  • lamba da baka sani ba
  • matsa maka ka yi abu ba tare da tunani ba

Idan ka ga ɗaya daga ciki, ka yi taka-tsantsan.

Yadda Ake Kare Kanka Daga Damfara a WhatsApp

1. Kada Ka Raba Bayananka na Sirri

Kada ka raba:

  • OTP
  • PIN
  • password
  • verification code

Ko da wanda ya nemi bayanin ya ce daga hukuma ne.

2. Kunna Two-Step Verification

Wannan yana ƙara tsaro ga WhatsApp ɗinka.

Yadda ake kunnawa:
Settings → Account → Two-step verification → Enable

3. Kulle Privacy Settings

Saita:

  • wanda zai ga hotonka
  • wanda zai ga status ɗinka
  • wanda zai iya saka ka a group

Wannan yana rage samun damfara.

4. Kada Ka Amince da Kowa Cikin Sauƙi

  • Ko da sakon ya zo daga aboki, ka tabbatar
  • Idan an nemi kuɗi, ka kira mutum da murya

5. Guji Tura Sakonni Ba Tabbaci

Idan ka samu sako:

  • mai tsoratarwa
  • ko mai yaudara

Kada ka tura shi zuwa wasu. Wannan yana taimaka wa masu damfara.

6. Report & Block Masu Damfara

WhatsApp yana da zaɓin:

  • Block
  • Report

Yi amfani da su domin kare kanka da sauran mutane.

Rawar Iyaye da Al’umma

Iyaye su:

  • koya wa ’ya’yansu yadda ake amfani da WhatsApp cikin tsaro
  • faɗakar da su game da damfara

Al’umma su:

  • rika wayar da kai
  • rika sanar da juna sabbin dabarun damfara

Me Zai Faru Idan Aka Yi Sakaci?

Idan aka yi sakaci:

  • ana iya sace account
  • ana iya rasa kuɗi
  • ana iya fallasa sirri

Kariya ta fi gyara.

Kammalawa

Damfara a WhatsApp gaskiya ce a wannan zamani, amma ana iya kauce mata idan mutum yana da ilimi da hankali. Ba kowane sako bane gaskiya, ba kowane alkawari bane na gaskiya.

Ta hanyar:

  • taka-tsantsan
  • kare bayananka
  • wayar da kai

za ka iya amfani da WhatsApp cikin aminci.

📌 Shawara

Ka raba wannan rubutu da:

  • iyalanka
  • abokanka
  • group ɗinka

Domin ilimi kariya ne.

We will be happy to hear your thoughts

Leave a reply

ADT TECH SOL
Logo