
Gabatarwa
A wannan zamani na fasaha, intanet ya zama wani muhimmin ɓangare na rayuwarmu ta yau da kullum. Muna amfani da shi wajen: mu’amala da mutane, banki da tura kuɗi, kasuwanci da kuma amfani da kafafen sada zumunta
Sai dai, tare da wannan ci gaba, satar bayanai ta hanyar phishing ta zama babbar barazana. saboda Mutane da dama suna rasa: bayanan sirrinsu, Kudaden su, da kuma accounts din email da social media din su, ba tare da sun sani ba. saboda haka
Wannan rubutu zai yi bayani dalla-dalla kan menene phishing, yadda ake aiwatar da shi, alamominsa, illolinsa, da kuma yadda zaka kare kanka.
Menene Phishing?
Phishing wata dabara ce da masu damfara (Scammers or Hackers ) ke amfani da ita wajen ruɗar mutane su bayar da bayanansu da kansu, ba tare da amfani da ƙarfi ko kutse kai tsaye ba.
Yawanci masu phishing suna kwaikwayon: banki, kamfanoni, kafafen sada zumunta, da ma hukumomi
Suna tura sakonni ko ƙirƙirar shafukan yanar gizo da suke kama da na gaskiya domin su sa mutum ya shigar da bayanan sirrin sa kamar su: password, PIN, OTP ko kuma bayanan ATM din sa
Dalilin da Yasa Phishing Ke Yawaita
Akwai dalilai da dama da suka sa phishing ke ƙara yawaita:
1. Yawaitar Masu Amfani da Intanet
Yawan mutane da ke amfani da intanet yana ƙaruwa, musamman waɗanda ba su da cikakken ilimin tsaro wato cybersecurity ko muce cyber awareness.
2. Sauƙin Aiwatar da Phishing
Masu damfara ba sa buƙatar ilimin fasaha mai zurfi. Sakon karya kaɗai na iya yaudarar mutum yamika bayanan sirrin sa ba tare da ya sani ba.
3. Rashin Wayar da Kai
Mutane da dama ba su san yadda phishing ke aiki ba, don haka suna faɗawa tarkonsa cikin sauƙi. saboda haka ne muka zabi muna yin rubutu akan ire iran wadan nan bayane domin wayar da kan al’ummar mu, kaima in kana so kabada taka gudun mawar sai kayi sharing domin wasu su amfana, don bari muciga ba da bayanin mu.
Yadda Ake Satar Bayanai Ta Hanyar Phishing
2. Ta Hanyar Email (Email Phishing)
Ana aika email da ke kama da na: banki ko wani kamfanin sadarwa ko kuma social media. a na roƙonka ka da cewa danna link ko ka shigar da bayananka don samun tallafi ko aikinyi da dai sauransu.

- Idan kaduba sender Email address zakaga ba official email din netflix bane
- Sannan idan ka sake dubu Subject na email din za kaga ana fadamaka cewa netfilix sunyi suspending dinka.
- Saboda kayi saurin danna link din ke cikin Email body, don daukan matakin gaggawa saboda kar su rufe maka account, Kana danna link din shekenan za su fara satar bayanan ka.

- Idan kaduba sender Email Body zaka link a jikin PDF, abinda suke so shine kayi download virus ko malware a wayar ka ko kwamfiyutar ka.
- Haka dai a Email Body harda lambar waya kamar ta gaske.
- Sannan Email Body na dauke da file, PDF wanda zai iya kasan cewa malicious file ne.
2. Ta Hanyar Sakonnin WhatsApp ko SMS
Sai kawai kaga an tura maka sako kamar: “Account ɗinka yana cikin haɗari” ko kuma kamar haka: “Sabunta bayananka yanzu”. Sannan kasani cewa Sakon yana zuwa da link da ke kai ka shafin bogi. inda ake so kasaka bayanan ka, da zarar kasaka shikenen hackers sun samu abinda suke so.
3. Ta Hanyar Fake Website
Ana ƙirƙirar website da ya yi kama da na gaske. Da zarar ka shigar da bayananka: za a adana su a yi amfani da su wajen satar account ɗinka,
Ga misali kamar haka:


Danna nan; Don sanin: Alamomin Fake Website: Yadda Zaka Gane Shafukan Bogi a Intanet
4. Ta Hanyar Kira (Voice Phishing)
Wani zai kira ka ya ce:
“Ni jami’in banki ne” Ko kuma wata hukuma Kamar irin EFCC da dai sauran su
Ya nemi bayananka cikin ladabi ko tsoratarwa.
Alamomin Phishing da Ya Kamata Ka Lura Da Su
Ga wasu manyan alamomi:
- sako mai cike da gaggawa
- buƙatar bayanai masu muhimmanci
- link daga wanda baka sani ba
- rubutu mai kurakurai
- alkawari ko tsoratarwa
Idan ka ga ɗaya daga cikin wadan nan abinda muka ambata toh, ka yi taka-tsantsan.
Illolin Phishing
Phishing na iya jawo:
- satar kuɗi
- satar identity
- rasa email ko social media account
- fallasa bayanan sirri
Wasu lokuta ma mutum ba zai gane abin da ya faru ba sai bayan an riga an cutar da shi.
Yadda Zaka Kare Kanka Daga Phishing
1. Kada Ka Taɓa Bada Bayananka
Kada ka raba:
- OTP
- PIN
- password
Ko da wanda ya nema ya ce daga hukuma ne.
2. Kada Ka Danna Link Din Da Ba Kada Tabbaci Akan Sa
Musamman daga:
- SMS
In ma zaka shiga website din ne toh kashiga ta hanyar rubuta adireshinsa da kanka.
3. Duba Adireshin Website (URL)
Ka tabbata URL ɗin:
- daidai ne
- babu ƙarin haruffa ko lambobi
- Sannan da mukulli ko babu? in da mukulli toh da alamun sahihanci, in ko babu toh da matsala

4. Kunna Two-Factor Authentication
Wannan kariya ce da ke hana masu damfara shiga account ɗinka ko da sun samu password.
5. Wayar da Kai ga Wasu
Faɗakar da:
- iyalai
- abokai
- yara da tsofaffi
Domin su ma su kare kansu.
Bambancin Phishing da Kutse (Hacking)
- Phishing: ana ruɗar mutum ya bayar da bayanai da kansa
- Hacking: ana amfani da fasaha kai tsaye wajen shiga tsarin wani
Phishing ya fi yaduwa saboda yana amfani da raunin ɗan Adam, ba fasaha kaɗai ba.
Rawar Cyber Awareness Wajen Rage Phishing
Idan mutane suna da ilimi:
- phishing zai ragu
- asarar kuɗi za ta ragu
- amincewa da intanet za ta ƙaru
Cyber Awareness hanya ce mafi inganci wajen yaƙar phishing.
Kammalawa
Phishing babbar barazana ce a duniyar intanet, amma ana iya kauce mata da ilimi, hankali, da taka-tsantsan. Ba kowane sako bane gaskiya, ba kowane email bane na gaske.
Idan ka koya gane dabarun phishing, za ka iya kare:
- kanka
- iyalanka
- kasuwancinka
📌 Shawara da kuma Taimako
Ka tura wannan ilimi zuwa ga:
- abokai
- iyalai
- al’ummarka
Domin ilimi kariya ne.